Sai fa sarki Hirudus ya ji labari, domin sunan Yesu ya riga ya shahara, har waɗansu suka ce, “Yahaya Maibaftisma ne aka tasa daga matattu, shi ya sa mu'ujizan nan suke aiki ta wurinsa.”
Ta haka ya shahara a cikin duk ƙasar Suriya. Aka kuwa kakkawo masa dukan marasa lafiya, masu fama da cuta iri iri, da masu shan azaba, da kuma masu aljannu, da masu farraɗiya, da shanyayyu, ya kuwa warkar da su.
Sa'ad da aka haifi Yesu a Baitalami ta ƙasar Yahudiya, a zamanin sarki Hirudus, sai ga waɗansu masana taurari daga gabas suka zo Urushalima, suna cewa,