Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Luka 6:45 - Littafi Mai Tsarki

45 Mutumin kirki kam ta kyakkyawar taskar zuciyarsa yakan yi abin kirki, mugu kuwa ta mummunar taskar zuciyarsa yakan yi mugun abu. Ai, abin da ya ci rai, shi mutum yake faɗa.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

45 Mutumin nagari yakan nuna abubuwa nagari daga cikin nagarta da yake a ɓoye a zuciyarsa, mugun mutum kuwa yakan nuna mugayen abubuwa daga muguntar da take a ɓoye a zuciyarsa. Gama baki yakan faɗa abin da ya cika zuciya ne.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Luka 6:45
31 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Tunane-tunanenka mafarin rai ne kansa, ka kiyaye su abin mallakarka ne mafi daraja.


Kada wata alfasha ta fita daga bakinku, sai dai irin maganar da ta kyautu domin ingantawa, a kuma yi ta a kan kari, domin ta sa alheri ga masu jinta.


Duk mai gaskatawa da ni, kamar yadda Nassi ya ce, ‘Daga zuciyarsa ne kogunan ruwan rai za su gudana.’ ”


Maganar Almasihu tă kahu a cikin zuciyarku a yalwace, kuna koya wa juna, kuna yi wa juna gargaɗi da matuƙar hikima ta wurin rairar waƙoƙin Zabura da na yabon Allah, kuna kuma raira waƙa ga Allah, kuna gode masa tun daga zuci.


Zunubi na cikin leɓunansu, maganganunsu na zunubi ne, Da ma a kama su saboda girmankansu, Domin suna la'antarwa, suna ƙarya!


A kullum maganarku ta zama mai ƙayatarwa, mai daɗin ji, domin ku san irin amsar da ta dace ku ba kowa.


Maganganun rashin tunani suke sa rauni mai zurfi kamar saran takobi, amma kalmomin mai hikima sukan warkar da raunuka.


Wannan shi ne alkawarin da zan yi da jama'ar Isra'ila, Bayan kwanakin nan, in ji Ubangiji, Wato, zan sa shari'una a birnin zuciyarsu, In kuma rubuta su a allon zuciyarsu. Zan kasance Allahnsu, Su kuma su kasance jama'ata.


kuna zance da junanku da kalmomin zabura, da waƙoƙin yabo, da waƙoƙi na ruhu, kuna raira waƙoƙi da zabura ga Ubangiji da yabo a zukatanku.


Me ya fi wannan zama abin murna? Mutum ya sami maganar da take daidai a lokacin da ya dace!


Masu girmankai sun kafa mini tarko, Sun shimfiɗa ragar igiya, Sun kuma kakkafa tarkuna a hanya don su kama ni.


Ji abin da suke fada! Harsunansu suna kama da takuba a bakinsu, Duk da haka suna ta tambaya, suna cewa, “Wa zai ji mu?”


Sai Bitrus ya ce, “Kai, Hananiya, ta ƙaƙa Shaiɗan ya cika zuciyarka, har ka yi wa Ruhu Mai Tsarki ƙarya, ka kuma ɓoye wani abu daga kuɗin gonar?


don ya zartar da hukunci kan kowa, yă kuma tabbatar wa marasa bin Allah dukan aikinsu na rashin bin Allah, da suka aikata ta hanyar rashin bin Allah, da kuma baƙaƙen maganganu da masu zunubi marasa bin Allah suka yi game da shi.”


Ko da yake ni ne mafi ƙanƙantar tsarkaka duka, ni aka ba wannan alheri in yi wa al'ummai bishara a kan yalwar Almasihu marar ƙididdiguwa,


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ