Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Luka 6:14 - Littafi Mai Tsarki

14 Su ne Bitrus, da ɗan'uwansa Andarawas, da Yakubu, da Yahaya, da Filibus, da Bartalamawas,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

14 Siman (wanda ya kira Bitrus), ɗan’uwansa Andarawus, Yaƙub, Yohanna, Filibus, Bartolomeyu,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Luka 6:14
23 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Da suka shiga birnin, suka hau soro inda suke zama, wato Bitrus, da Yahaya, da Yakubu, da Andarawas, da Filibus, da Toma, da Bartalamawas, da Matiyu, da Yakubu na Halfa, da Saminu Zaloti, da kuma Yahuza na Yakubu.


Da ya ci gaba sai ya ga waɗansu mutum biyu, su kuma 'yan'uwa ne, Yakubu ɗan Zabadi, da ɗan'uwansa Yahaya, suna cikin jirgi tare da ubansu Zabadi, suna gyaran tarunansu. Sai ya kira su.


Yana tafiya a bakin Tekun Galili ke nan, sai ya ga waɗansu 'yan'uwa biyu, Saminu da ake kira Bitrus, da ɗan'uwansa Andarawas, suna jefa taru a teku, don su masunta ne.


Daga Saminu Bitrus, bawan Yesu Almasihu, manzonsa kuma, zuwa ga waɗanda aka yi wa baiwar bangaskiya mai daraja iri ɗaya da tamu, albarkacin adalcin Allahnmu da Mai Cetonmu Yesu Almasihu.


har ma ya sare Yakubu ɗan'uwan Yahaya da takobi.


Sai Filibus ya ce masa, “Ya Ubangiji, ka nuna mana Uban, bukatarmu ta biya ke nan.”


Sai Andarawas ɗan'uwan Bitrus ɗaya daga cikin almajiransa, ya ce masa,


Da Yesu ya ɗaga kai ya hango babban taro yana doso shi, sai ya ce wa Filibus, “Ina za mu sayo gurasar da mutanen nan za su ci?”


Filibus ya sami Nata'ala, ya ce masa, “Mun sami wanda Musa ya rubuta labarinsa a Attaura, annabawa kuma suka rubuta labarinsa, wato Yesu Banazare, ɗan Yusufu.”


haka ma Yakubu da Yahaya 'ya'yan Zabadi, abokan sabgar Bitrus. Sai Yesu ya ce wa Bitrus, “Kada ka ji tsoro. Nan gaba mutane za ka riƙa kamowa.”


Da Bitrus ya ga haka, sai ya fāɗi a gaban Yesu ya ce. “Ya Ubangiji, wane ni da za ka tsaya kusa da ni, domin ni mutum ne mai zunubi.”


Sai ya ɗauki Bitrus, da Yakubu, da Yahaya, ya kuma fara jin wahala gaya, yana damuwa ƙwarai.


Bayan kwana shida Yesu ya ɗauki Bitrus, da Yakubu, da Yahaya, ya kai su kan wani dutse mai tsawo, su kaɗai. Sai kamanninsa ya sāke a gabansu,


Bai bar kowa ya bi shi ba sai Bitrus, da Yakubu, da kuma Yahaya ɗan'uwan Yakubu.


Da fitarsu daga majami'a, sai suka shiga gidan su Bitrus da Andarawas, tare da Yakubu da Yahaya.


Da ya ci gaba kaɗan, sai ya ga Yakubu ɗan Zabadi, da ɗan'uwansa Yahaya, suna cikin jirginsu suna gyaran taruna.


da Filibus, da Bartalamawas, da Toma, da Matiyu mai karɓar haraji, da Yakubu ɗan Halfa, da Yahuza,


To, ga sunayen manzannin nan goma sha biyu. Da fari, Saminu, wanda ake kira Bitrus, da ɗan'uwansa Andarawas, da Yakubu ɗan Zabadi, da ɗan'uwansa Yahaya,


Da gari ya waye ya kira almajiransa, ya zaɓi goma sha biyu a cikinsu, ya ce da su manzanni.


da Matiyu, da Toma, da Yakubu ɗan Halfa, da Saminu, wanda ake ce da shi Zaloti,


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ