Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Luka 6:1 - Littafi Mai Tsarki

1 Wata rana ran Asabar, yana ratsa gonakin alkama, sai almajiransa suka zāgi alkamar, suna murtsukewa suna ci.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

1 A wata ranar Asabbaci, Yesu yana bi ta gonakin hatsi, sai almajiran suka fara kakkarya kan hatsi suna murjewa a hannuwansu suna ci.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Luka 6:1
10 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sa'ad da kuka shiga hatsin maƙwabcinku da yake tsaye, kun iya ku yi murmuren tsabar da hannunku, amma kada ku sa wa hatsin maƙwabcinku lauje.”


Za su yi muhimmin taro a rana ta fari. Ba za su yi aiki mai wuya a ranar ba.


“Za ku yi kwana bakwai kuna cin abinci marar yisti. A rana ta fari za ku fitar da yisti daga cikin gidajenku, gama duk wanda ya ci abin da aka sa wa yisti tun daga rana ta fari har zuwa ta bakwai za a fitar da shi daga cikin Isra'ila.


“Sai ku ƙirga mako bakwai, wato ku fara ƙirga mako bakwai ɗin daga lokacin da kuka fara sa lauje don ku yanke hatsinku da suke tsaye.


Za su ƙidaya mako bakwai daga kashegarin Asabar da suka kawo damin hadaya ta kaɗawa domin miƙa wa Ubangiji.


Ba wanda zai so shan sabon ruwan inabin bayan ya sha tsohon, don ya ce, ‘Ai, tsohon yana da kyau.’ ”


A wata Asabar kuma ya shiga majami'a, yana koyarwa. Akwai kuwa wani mutum a ciki wanda hannunsa na dama ya shanye.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ