Maganar nan ta tashi saboda 'yan'uwan ƙaryar nan ne, da aka shigo da su a asirce, waɗanda suka saɗaɗo su yi ganganen 'yancinmu da muke da shi ta wurin Almasihu Yesu, don dai su sa mu bauta.
Ba kuma mai ɗura sabon ruwan inabi a tsofaffin salkuna. In ma an ɗura, sai salkunan su fashe, ruwan inabin ya zube, salkunan kuma su lalace. Sabon ruwan inabi, ai, sai sababbin salkuna. Ta haka an tserar da duka biyu ke nan.”