Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Luka 5:21 - Littafi Mai Tsarki

21 Sai malaman Attaura da Farisiyawa suka fara wuswasi cewa, “Wane ne wannan da yake maganar saɓo? Wa yake iya gafarta zunubi banda Allah shi kaɗai?”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

21 Farisiyawa da malaman dokoki suka fara yin tunani a zukatansu, “Wane ne wannan mutum da yake saɓo haka? Wa zai iya gafarta zunubai, in ba Allah kaɗai ba?”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Luka 5:21
23 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Duk da haka, ni ne Allah wanda ya shafe zunubanku, Na kuwa yi haka saboda yadda nake. Ba zan ƙara tunawa da zunubanku kuma ba.


Yahudawa suka amsa suka ce, “Ba don wani aiki nagari za mu jajjefe ka ba, sai don sāɓo, don kai, ga ka mutum, amma kana mai da kanka Allah.”


Masu ci tare da shi kuwa suka fara ce wa juna, “Wannan kuwa wane ne wanda har yake gafarta zunubai?”


Sai babban firist ya kyakketa tufafinsa, ya ce, “Ya yi saɓo! Wace shaida kuma za mu nema? Yanzu kun ji saɓon da ya yi!


Sa'an nan na hurta zunubaina gare ka, Ban ɓoye laifofina ba. Na ƙudurta in hurta su gare ka, Ka kuwa gafarta dukan laifofina.


za a kuwa kashe shi. Duk Ba'isra'ile ko baƙon da yake zaune cikin Isra'ilawa wanda ya saɓi Allah, sai taron jama'a su jajjefe shi da duwatsu ya mutu.


Wa zai ɗora wa zaɓaɓɓun Allah laifi? Allah ne yake kuɓutar da su!


Ya Ubangiji, ka ji mu. Ya Ubangiji, ka garfarce mu. Ya Ubangiji, ka saurare mu, ka yi wani abu saboda sunanka. Ya Allahna, kada ka yi jinkiri domin da sunanka ake kiran birninka da jama'arka.”


Ubangiji Allahnmu mai jinƙai ne mai gafara, amma mu, mun tayar masa.


Na shafe zunubanka kamar baƙin girgije, Da girgije kuma zan rufe laifofinka Ka komo wurina, ni ne na fanshe ka.”


Ubangiji ya ce, “Yanzu fa, bari mu daidaita al'amarinmu. Duk kun yi ja wur da zunubi, amma zan wanke ku, ku yi fari fat kamar auduga. Zai yiwu zunubinku ya sa ku zama ja wur, amma za ku yi fari fat kamar farin ulu.


Amma kakan gafarta mana, Domin mu zama masu tsoronka.


Ya gafarta dukan zunubaina, Ya kuma warkar da dukan cuce-cucena.


Wata rana na koyarwa, waɗansu Farisiyawa kuwa da masanan Attaura da suka fito daga kowane gari na ƙasar Galili, da na ƙasar Yahudiya, daga kuma Urushalima, suna nan a zaune. Ikon Ubangiji na warkarwa kuwa yana nan.


Sai waɗansu malaman Attaura suka ce a ransu, “Wannan mutum, ai, saɓo yake!”


Zai sāke jin juyayinmu, Ya tattake muguntarmu a ƙarƙashin ƙafafunsa. Za ka jefar da zunubanmu a cikin zurfin teku.


Ka sa su zama kamar tattakar da iska take kwashewa, Kamar waɗanda mala'ikan Ubangiji yake korarsu!


Ku yi aikin da zai nuna tubanku, kada ma ku ko fara cewa a ranku Ibrahim ne ubanku. Ina dai gaya muku Allah yana da iko ya halitta wa Ibrahim 'ya'ya daga duwatsun nan.


Da Yesu ya gane wuswasinsu, ya amsa musu ya ce, “Don me kuke wuswasi haka a zuciyarku?


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ