Sai aka kawo masa wani shanyayye, kwance a gado. Da Yesu ya ga bangaskiyarsu, sai ya ce wa shanyayyen, “Ɗana, ka yi farin ciki, an gafarta maka zunubanka.”
To, amma wani zai ce, “Ai, kai kana da bangaskiya, ni kuwa sai aikatawa.” To, nuna mini bangaskiya, taka ba tare da aikatawa ba, ni kuma in nuna maka aikatawata, tabbatar bangaskiyata.
Ya ce, “Kada ka sa hannunka a kan saurayin, kada kuwa ka yi masa wani abu, gama yanzu na sani kai mai tsoron Allah ne, da yake ba ka ƙi ba da ɗanka, tilonka, a gare ni ba.”