Da ganin Yesu sai ya ƙwala ihu, ya faɗi a gabansa, ya ɗaga murya ya ce, “Ina ruwanka da ni, ya Yesu Ɗan Allah Maɗaukaki? Ina roƙonka, kada ka yi mini azaba.”
Ni Yahaya, ni ne na ji, na kuma ga waɗannan abubuwa. Sa'ad da kuwa na ji su, na kuma gan su, sai na fāɗi a gaban mala'ikan da ya nuna mini su, domin in yi masa sujada.
Da ya ɗauki littafin, rayayyun halittan nan guda huɗu, da dattawan nan ashirin da huɗu, suka fāɗi gaban Ɗan Ragon, kowannensu yana riƙe da molo, da tasar zinariya a cike da turare, waɗanda suke addu'o'in tsarkaka.
sai dattawan nan ashirin da huɗu suka fāɗi a gaban wanda yake a zaune a kan kursiyin, su yi masa sujada, shi da yake a raye har abada abadin, su kuma ajiye kambinsu a gaban kursiyin, suna waƙa, suna cewa,
Da suka shiga gidan kuwa, sai suka ga ɗan yaron, tare da uwa tasa Maryamu, suka fāɗi gabansa suka yi masa sujada. Sa'an nan suka kwance kayansu, suka miƙa masa gaisuwar zinariya, da lubban, da mur.
Mutane suka buɗe alabensu suna zazzage zinariya, Suna auna azurfa a kan ma'auni. Suka yi jingar maƙerin zinariya don ya yi musu gunki, Sa'an nan suka rusuna suka yi masa sujada!
Ubangiji ya ce wa Isra'ila, “Dukiyar Masar da ta Habasha za ta zama taku, Dogayen mutanen Seba kuma za su zama bayinku, Za su bi ku suna a ɗaure da sarƙoƙi. Za su rusuna a gabanku su tuba, su ce, ‘Allah yana tare da ku, shi kaɗai ne Allah.’ ”