Sai fa sarki Hirudus ya ji labari, domin sunan Yesu ya riga ya shahara, har waɗansu suka ce, “Yahaya Maibaftisma ne aka tasa daga matattu, shi ya sa mu'ujizan nan suke aiki ta wurinsa.”
Amma ya tafi, ya shiga sanar da maganar, yana baza labarin al'amarin ko'ina, har ya zamana Yesu bai ƙara shiga wani gari a sarari ba, sai ya zauna a waje a wuraren da ba kowa. Mutane kuwa suka yi ta zuwa wurinsa daga ko'ina.