21 Sai ya fara ce musu, “Yau Nassin nan ya cika a kunnenku.”
21 Sai ya fara ce musu, “A yau, Nassin nan, ya cika a kunnenku.”
Amma ta haka Allah ya cika faɗar da ya riga ya yi ta bakin annabawa duka, cewa Almasihunsa zai sha wuya.
Lalle a kansu ne aka cika annabcin Ishaya cewa, “ ‘Za ku ji kam, amma ba za ku fahimta ba faufau, Za ku kuma gani, amma ba za ku gane ba faufau,
Kuna ta nazarin Littattafai, don a tsammaninku a cikinsu za ku sami rai madawwami, alhali kuwa su ne suke shaidata.
Ya rufe littafin ya mayar wa mai hidima, ya zauna. Duk waɗanda suke cikin majami'a suka zuba masa ido.
Duk suka yabe shi, suna mamakin maganarsa ta alheri da ya faɗa, har suka ce, “Ashe, wannan ba ɗan Yusufu ba ne?”