Ya aike ni in yi shela, Cewa lokaci ya yi Da Ubangiji zai ceci mutanensa, Ya kuma ci nasara a kan abokan gābansu. Ya aike ni domin in ta'azantar da masu makoki,
Sa'ad da shekara ta hamsin ta murnar Isra'ilawa ta kewayo, za a haɗa gādonsu da na kabilan mutanen da suka aura, da haka za a ɗebe gādonsu daga gādon kabilar kakanninmu.”
Ubangiji ya ce, “Ga bawana, wanda na ƙarfafa, Wanda na zaɓa, wanda nake jin daɗinsa. Na cika shi da ikona, Zai kuwa kawo shari'ar gaskiya ga dukan al'ummai.