Luka 4:18 - Littafi Mai Tsarki18 “Ruhun Ubangiji yana tare da ni, Domin yā shafe ni in yi wa matalauta bishara. Ya aiko ni in yi shelar saki ga ɗaurarru, In kuma buɗe wa makafi ido, In kuma 'yanta waɗanda suke a danne, အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202018 “Ruhun Ubangiji yana kaina, domin ya shafe ni, in yi wa matalauta wa’azin bishara. Ya aiko ni in yi shelar ’yanci ga ’yan kurkuku, in kuma buɗe idanun makafi, in ba da ’yanci ga waɗanda aka danne. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Ni kaina na iza Sairus ya yi wani abu, Don ya cika nufina ya daidaita al'amura. Zan miƙar da kowace hanyar da zai yi tafiya a kai. Zai sāke gina birnina, wato Urushalima, Ya kuma 'yantar da mutanena da suke bautar talala. Ba wanda ya yi ijara da shi, ko ya ba shi rashawa don ya yi wannan.” Ubangiji Mai Runduna ne ya faɗi wannan.