tun da yake bai rangwanta wa mutanen tun can dā dā kuma ba, amma ya kiyaye Nuhu mai wa'azin adalci, da waɗansu mutum bakwai, sa'ad da ya aiko da Ruwan Tsufana zuwa a cikin duniyar nan ta marasa bin Allah,
wato, waɗanda dā ba su bi ba, sa'ad da Allah ya yi jira da haƙuri a zamanin Nuhu, a lokacin sassaƙar jirgin nan, wanda a cikinsa mutane kaɗan, wato takwas suka kuɓuta ta ruwa.
Ta wurin bangaskiya Nuhu, da Allah ya yi masa gargaɗi a kan al'amuran da ba a gani ba a lokacin, yana tsoron Allah, ya sassaƙa jirgi, don ceton iyalin gidansa, ta wurin bangaskiya kuma ya tabbatar wa duniya laifinta, har ya zama magājin adalcin Allah, wanda yake samuwa ta wurin bangaskiya.
Allah kuwa ya tuna da Nuhu da dukan dabbobin gida da na jeji waɗanda suke cikin jirgi tare da shi. Allah ya sa iska ta hura bisa duniya, ruwaye suka janye.
Ubangiji ya shafe kowane mai rai wanda yake bisa ƙasa, da mutum, da dabba, da masu rarrafe, da tsuntsayen sararin sama, an shafe su daga duniya. Nuhu kaɗai aka bari, da waɗanda suke tare da shi cikin jirgi.