Daga baya kuma ɗan'uwansa ya fito, hannunsa na riƙe da diddigen Isuwa, saboda haka aka raɗa masa suna Yakubu. Ishaku yana da shekara sittin sa'ad da ya haife su.
Ya kuma yi masa alkawari game da kaciya. Ta haka, da Ibrahim ya haifi Ishaku, ya yi masa kaciya a rana ta takwas. Ishaku ya haifi Yakubu, Yakubu kuma ya haifi kakanninmu sha biyun nan.
Joshuwa kuwa ya ce wa mutane duka, “Ga abin da Ubangiji Allah na Isra'ila ya ce, ‘A zamanin dā kakanninku, su Tera, mahaifin Ibrahim, da Nahor, suna zaune a hayin Yufiretis. Suka bauta wa gumaka.