Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Luka 3:23 - Littafi Mai Tsarki

23 Yesu kuwa sa'ad da ya fara koyarwa, yana da shekara wajen talatin. An ɗauke shi a kan, wai shi ɗan Yusufu ne, wanda yake ɗan Heli,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

23 To, Yesu kansa yana da shekaru kusan talatin da haihuwa sa’ad da ya fara aikinsa. An ɗauka shi ɗan Yusuf ne, ɗan Heli,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Luka 3:23
20 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ashe, wannan ba ɗan masassaƙin nan ba ne? Uwa tasa ba sunanta Maryamu ba? 'Yan'uwansa kuwa ba su ne Yakubu, da Yusufu, da Saminu, da kuma Yahuza ba?


su ƙidaya daga mai shekara talatin zuwa hamsin, wato waɗanda suka isa su yi aiki a alfarwa ta sujada.


Ya Tiyofalas, tarihin nan na farko wanda na rubuta, ya shafi dukan abubuwan da Yesu ya fara yi, da kuma waɗanda ya fara koyarwa,


Suka ce, “Ashe, wannan ba Yesu ba ne, ɗan Yusufu, wanda uwa tasa da ubansa duk mun san su? To, yaya yanzu zai ce, ‘Na sauko ne daga sama’?”


Duk suka yabe shi, suna mamakin maganarsa ta alheri da ya faɗa, har suka ce, “Ashe, wannan ba ɗan Yusufu ba ne?”


Shin, wannan ba shi ne masassaƙin nan ba, ɗan Maryamu, ɗan'uwan su Yakubu, da Yusufu, da Yahuza, da kuma Saminu? 'Yan'uwansa mata kuma ba ga su tare da mu ba?” Suka yi tuntuɓe sabili da shi.


Tun daga lokacin nan, Yesu ya fara wa'azi, yana cewa, “Ku tuba domin Mulkin Sama ya kusato.”


Yakubu ya haifi Yusufu mijin Maryamu wadda ta haifi Yesu, wanda ake kira Almasihu.


Yusufu yana da shekara talatin lokacin da ya kama aiki a wurin Fir'auna, Sarkin Masar. Yusufu kuwa ya fita daga gaban Fir'auna ya ratsa dukan ƙasar Masar.


Eliyakim ɗan Malaya, Malaya ɗan Mainana, Mainana ɗan Matata, Matata ɗan Natan, Natan ɗan Dawuda,


Yesse ya haifi sarki Dawuda. Dawuda kuma ya haifi Sulemanu (wanda uwa tasa dā matar Uriya ce),


Littafin asalin Yesu Almasihu, ɗan Dawuda, zuriyar Ibrahim ke nan.


Dawuda ya ci sarauta yana da shekara talatin. Ya yi shekara arba'in yana sarauta.


Da suka gan shi suka yi mamaki, sai uwa tasa ta ce masa, “Ya kai ɗana, yaya ka yi mana haka? Ga shi nan, ni da babanka muna ta nemanka duk ranmu a ɓace.”


Filibus ya sami Nata'ala, ya ce masa, “Mun sami wanda Musa ya rubuta labarinsa a Attaura, annabawa kuma suka rubuta labarinsa, wato Yesu Banazare, ɗan Yusufu.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ