“Amma suka yi maka rashin biyayya, suka tayar maka, Suka juya wa dokokinka baya, Suka karkashe anna bawan da suka faɗakar da su, Waɗanda suka faɗa musu su juyo gare ka. Suka yi ta saɓa maka lokaci lokaci.
Sai suka yi ta yi wa manzannin Allah ba'a, suka raina maganarsa, suka yi wa annabawansa ba'a, sai Ubangiji ya husata da jama'arsa don abin ya kai intaha.
Banda wannan kuma Manassa ya kashe adalai har ya cika Urushalima daga wannan gefe zuwa wancan da jininsu, banda zunubin da ya sa mutanen Yahuza su yi, har suka aikata abin da yake mugu a gaban Ubangiji.