Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Luka 3:16 - Littafi Mai Tsarki

16 sai Yahaya ya amsa wa dukansu ya ce, “Ni kam, da ruwa nake yi muku baftisma, amma wani yana zuwa wanda ya fi ni girma, wanda ko maɓallin takalminsa ma ban isa in ɓalle ba. Shi ne zai yi muku baftisma da Ruhu Mai Tsarki, da kuma wuta.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

16 Yohanna ya amsa musu duka ya ce, “Ina muku baftisma da ruwa. Amma wani wanda ya fi ni iko yana zuwa, ban ma isa in kunce igiyar takalmansa ba. Shi zai yi muku baftisma da Ruhu Mai Tsarki da wuta kuma.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Luka 3:16
24 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

domin Yahaya kam, da ruwa ya yi baftisma, amma kafin 'yan kwanaki da Ruhu Mai Tsarki za a yi muku baftisma.”


“Ni dai, da ruwa nake muku baftisma, shaidar tubarku, amma mai zuwa bayana, ya fi ni girma, wanda ko takalmansa ma ban isa in riƙe ba. Shi ne zai yi muku baftisma da Ruhu Mai Tsarki, da kuma wuta.


Dā kam, ban san shi ba, sai dai wanda ya aiko ni in yi baftisma da ruwa, shi ne ya ce mini, ‘Wanda ka ga Ruhun na sauko masa, yana kuma kasance a kansa, shi ne mai yin baftisma da Ruhu Mai Tsarki.’


Sai Yahaya ya amsa musu ya ce, “Ni kam, da ruwa nake baftisma, amma da wani nan tsaye a cikinku wanda ba ku sani ba,


Dukanmu an yi mana baftisma ta wurin Ruhu guda, mu zama jiki guda, Yahudawa ko al'ummai, bayi ko 'ya'ya, dukanmu kuwa an shayar da mu Ruhu guda.


Sulusi ɗayan da ya ragu kuwa zan tura cikin wuta, Zan tace su da wuta kamar yadda akan tace azurfa, Zan gwada su kamar yadda akan gwada zinariya. Za su kira gare ni, Zan kuwa amsa musu, Zan ce, ‘Su jama'ata ne,’ Su kuma za su ce, ‘Ubangiji shi ne Allahnmu.’ ”


Amma Allah zai ƙara aiko mana da Ruhunsa. Ƙasar da ta zama marar amfani za ta komo mai dausayi, gonaki kuma za su ba da amfani mai yawa.


Ta wurin ikonsa Ubangiji zai shara'anta al'ummar, ya kuma tsarkake ta, ya wanke laifin Urushalima, har da na jinin da aka zubar a can.


Ku kasa kunne lokacin da nake tsauta muku, zan ba ku shawara mai kyau, mu yi tarayya cikin ilimina.


Da yake an ɗaukaka shi a dama ga Allah, ya kuma sami cikar alkawarin nan na baiwar Ruhu Mai Tsarki daga wurin Uba, sai ya zubo da wannan da kuke gani, kuke kuma ji.


Duk mai gaskatawa da ni, kamar yadda Nassi ya ce, ‘Daga zuciyarsa ne kogunan ruwan rai za su gudana.’ ”


Bitrus na a cikin wannan magana, sai Ruhu Mai Tsarki ya sauko wa dukan masu jinta.


Zan yayyafa muku tsabtataccen ruwa, za ku kuwa tsarkaka daga dukan ƙazantarku, da kuma daga dukan gumakanku.


Ƙwaryar shiƙarsa na hannunsa, zai kuwa share masussukarsa sarai sarai, ya taro alkamarsa ya sa a rumbunsa, amma ɓuntun, sai ya ƙone a wutar marar kasuwa.”


shi ne mai zuwa bayana, wanda ko maɓallin takalminsa ma, ban isa in ɓalle ba.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ