Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Luka 3:14 - Littafi Mai Tsarki

14 Waɗansu soja ma suka tambaye shi, “To, mu fa, me za mu yi?” Sai ya ce musu, “Kada ku yi wa kowa ƙwace ko ƙazafi. Ku dai dangana da albashinku.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

14 Sai waɗansu sojoji suka tambaye shi, “Mu fa? Me ya kamata mu yi?” Sai ya amsa ya ce, “Kada ku ƙwace kuɗin mutane, kada kuma ku yi shaidar ƙarya. Ku yi haƙuri da abin da ake biyanku.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Luka 3:14
15 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ba cewa, ina kukan rashi ba ne, domin na koyi yadda zan zauna da wadar zuci a cikin kowane irin hali da nake.


“Kada ku yi sata, ko ku cuci wani, ko ku yi ƙarya.


Kada ku baza rahoton ƙarya. Kada wani ya haɗa baki da mugu ya zama munafukin mashaidi.


Sai Zakka ya miƙe, ya ce wa Ubangiji, “Ya Ubangiji, ka ga, rabin mallakata zan ba gajiyayyu. Kowa na zalunta kuwa, zan mayar masa da ninki huɗu.”


Sai na ji wata murya mai ƙara a Sama tana cewa, “A yanzu fa, ceto, da ƙarfi, da mulki na Allahnmu, da kuma ikon Almasihunsa sun bayyana, don an jefa mai ƙarar 'yan'uwanmu a ƙasa, shi da yake ƙararsu dare da rana a gun Allahnmu.


Haka kuma, manyan mata su kasance masu keɓaɓɓen hali, ba masu yanke, ko masu jarabar giya ba, su zamana masu koyar da kyakkyawan abu,


don ku zama marasa abin zargi, sahihai, 'ya'yan Allah marasa aibu, a zamanin mutane karkatattu, kangararru, waɗanda kuke haskakawa a cikinsu kamar fitilu a duniya,


Da mala'ikan da ya yi masa magana ya tafi, ya kira barorinsa biyu, da kuma wani soja mai ibada daga cikin waɗanda suke yi masa hidima kullum.


Yana shiga Kafarnahum ke nan, sai wani jarumi ya zo gunsa ya roƙe shi,


Sai taron suka tambaye shi suka ce, “Me za mu yi ke nan?”


Ya ce musu, “Kada ku karɓi fiye da abin da aka umarce ku.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ