Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Luka 23:7 - Littafi Mai Tsarki

7 Da ya ji Yesu a ƙarƙashin mulkin Hirudus yake, sai ya aika da shi wurin Hirudus, don shi ma yana Urushalima a lokacin.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

7 Da ya ji cewa, Yesu yana ƙarƙashin mulkin Hiridus ne, sai ya aika da shi zuwa wurin Hiridus, don a lokacin Hiridus yana Urushalima.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Luka 23:7
9 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

A shekara ta goma sha biyar ta mulkin Kaisar Tibariyas, Buntus Bilatus yana mulkin Yahudiya, Hirudus yana sarautar Galili, ɗan'uwansa Filibus yana sarauta Ituriya da Tarakunitas, Lisaniyas kuma yana sarautar Abiliya,


Nan take waɗansu Farisiyawa suka zo suka ce masa, “Ai, sai ka tashi, ka fita daga nan, gama Hirudus yana son kashe ka.”


A lokacin nan sarki Hirudus ya ji labarin shaharar Yesu.


Don dā ma Hirudus ya kama Yahaya ya ɗaure shi, ya sa shi kurkuku saboda Hirudiya, matar ɗan'uwansa Filibus.


To, da ranar haihuwar Hirudus ta kewayo, sai 'yar Hirudiya ta yi rawa a gaban taron, har ta gamshi Hirudus,


Sai fa sarki Hirudus ya ji labari, domin sunan Yesu ya riga ya shahara, har waɗansu suka ce, “Yahaya Maibaftisma ne aka tasa daga matattu, shi ya sa mu'ujizan nan suke aiki ta wurinsa.”


To, sarki Hirudus ya ji duk abin da ake yi, ya kuwa damu ƙwarai, don waɗansu suna cewa Yahaya ne aka tasa daga matattu.


Da Bilatus ya ji haka, ya tambaya ko mutumin nan Bagalile ne.


Gama hakika Hirudus da Buntus Bilatus sun haɗa kai a birnin nan tare da al'ummai da jama'ar Isra'ila gāba da Yesu Baranka mai tsarki, wanda ka maishe shi Almasihu.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ