6 Da Bilatus ya ji haka, ya tambaya ko mutumin nan Bagalile ne.
6 Da Bilatus ya ji haka, sai ya yi tambaya, “Ko shi mutumin Galili ne?”
Bayansa kuma, a lokacin ƙirgen mutane, wai shi Yahuza Bagalile ya ɓullo, ya zuga waɗansu suka yi turu, suka bi shi. Shi ma ya hallaka, duk mabiyansa ma aka warwatsa su.
Nan take waɗansu da suke a wurin suka ba shi labarin Galilawan da Bilatus ya sa aka kashe, har jininsu ya gauraya da na yankan da suka yi na hadaya.
To, Bitrus kuwa yana zaune a tsakar gida a waje, sai wata baranya ta zo ta tsaya a kansa, ta ce, “Kai ma, ai, tare kake da Yesu Bagalile!”
Sai suka fara matsa masa lamba, suna cewa, “Yana ta da hankalin jama'a, yana koyarwa a dukan ƙasar Yahudiya, tun daga ƙasar Galili har zuwa nan.”
Da ya ji Yesu a ƙarƙashin mulkin Hirudus yake, sai ya aika da shi wurin Hirudus, don shi ma yana Urushalima a lokacin.