38 Sama da shi kuma aka yi wani rubutu cewa, “Wannan shi ne Sarkin Yahudawa.”
38 Bisa da shi kuma akwai rubutun da ya ce, Wannan shi ne Sarkin Yahudawa.
Aka kuma rubuta sanarwar laifinsa sama da shi, wato “Sarkin Yahudawa.”
A daidai kansa aka kafa sanarwar laifinsa cewa, “Wannan shi ne Yesu, Sarkin Yahudawa.”
Sai Bilatus ya tambaye shi ya ce, “Ashe, kai ɗin nan, kai ne Sarkin Yahudawa?” Yesu ya amsa ya ce, “Yadda ka faɗa.”
Almasihun nan, Sarkin Isra'ila, yă sauko mana daga gicciyen yanzu, mu kuwa mu gani mu ba da gaskiya.” Waɗanda aka gicciye tare da shi su ma suka zazzage shi.
Suka yi ta zuwa wurinsa, suna cewa, “Ranka ya daɗe, Sarkin Yahudawa!” suna ta marinsa.
Sai suka fara gaishe shi, “Ranka ya daɗe, Sarkin Yahudawa!”
To, sai Yesu ya tsaya a gaban mai mulki, mai mulkin kuma ya tambaye shi, “Ashe, kai ɗin nan kai ne Sarkin Yahudawa?” Yesu ya ce masa, “Yadda ka faɗa.”
“Ina wanda aka haifa Sarkin Yahudawa? Domin mun ga tauraronsa a gabas, mun kuma zo mu yi masa sujada.”