36 Soja kuma suka yi masa ba'a, suka matso, suka miƙa masa ruwan tsami,
36 Sojoji su ma, suka zo suka yi masa ba’a. Suka miƙa masa ruwan tsami.
Sa'ad da na ji yunwa, sai suka ba ni dafi, Sa'ad da na ji ƙishi, sai suka ba ni ruwan tsami.
Sai nan da nan ɗaya daga cikinsu ya yiwo gudu, ya ɗauko soso ya jiƙa shi da ruwan tsami, ya soka a sanda, ya miƙa masa yă sha.
Sai ɗayansu ya yiwo gudu, ya jiƙo wani soso da ruwan tsami, ya soka a sanda, ya miƙa masa yă sha, yana cewa, “Bari mu gani ko Iliya zai zo ya sauko da shi.”
suka miƙa masa ruwan inabi gauraye da wani abu mai ɗaci yă sha, amma da ya ɗanɗana sai ya ƙi sha.
Sai Hirudus da sojansa suka wulakanta shi, suka yi masa ba'a, da suka sa masa tufafi masu ƙawa kuma, suka mai da shi wurin Bilatus.