Ya sāke faɗa musu, a faɗa ta uku, “Ta wane hali? Wane mugun abu ya yi? Ai, ban sami dalilin kisa a gare shi ba. Saboda haka, zan yi masa bulala in sake shi.”
Amma Bulus ya ce musu, “Ai, a fili suka daddoke mu, ba ko bin ba'asi, mu ma da muke Romawa bisa ga 'yangaranci, suka jefa mu a kurkuku, yanzu kuma sā fitar da mu a ɓoye? Sai dai su zo da kansu su fito da mu.”
Amma aka yi masa rauni saboda zunubanmu, Aka daddoke shi saboda muguntar da muka aikata. Hukuncin da ya sha ya 'yantar da mu, Dūkan da aka yi ta yi masa, ya sa muka warke.