1 Duk taronsu sai suka tashi, suka kai shi gaban Bilatus.
1 Sai dukan majalisa suka tashi, suka kai shi gaban Bilatus.
Da gari ya waye sai majalisar shugabannin jama'a ta haɗu, da manyan firistoci da kuma malaman Attaura. Suka kai shi ɗakin majalisarsu suka ce,
Sai suka ce, “Wace shaida kuma za mu nema? Ai, mun ji da kanmu daga bakinsa.”
Gama hakika Hirudus da Buntus Bilatus sun haɗa kai a birnin nan tare da al'ummai da jama'ar Isra'ila gāba da Yesu Baranka mai tsarki, wanda ka maishe shi Almasihu.