9 Suka ce masa, “Ina kake so mu shirya?”
9 Suka tambaye shi suka ce, “Ina kake so mu je mu yi shirin?”
Sai Yesu ya aiki Bitrus da Yahaya, ya ce musu, “Ku je ku shirya mana Jibin Ƙetarewa mu ci.”
Ya ce musu, “Ga shi, da shigarku gari, za ku gamu da wani mutum ɗauke da tulun ruwa. Ku bi shi har zuwa cikin gidan da ya shiga.
Sai Yesu ya fara yi musu magana da misalai ya ce, “Wani mutum ne ya yi garkar inabi, ya shinge ta, ya haƙa ramin matse inabin, ya kuma gina wata 'yar hasumiyar tsaro. Ya ba waɗansu manoma sufurin garkar, sa'an nan ya tafi wata ƙasa.