Nan da nan sai zakara ya yi cara ta biyu. Bitrus kuwa ya tuna da maganar da Yesu ya faɗa masa cewa, “Kafin zakara ya yi cara ta biyu, za ka yi musun sanina sau uku.” Ko da ya tuno haka, sai ya fashe da kuka.
“Zan cika zuriyar Dawuda da mutanen Urushalima da ruhun tausayi da na addu'a. Za su dubi wanda suka soke shi, har ya mutu. Za su yi makoki dominsa kamar waɗanda aka yi musu rasuwar ɗan farinsu.
“Na ji Ifraimu yana baƙin ciki, yana cewa, ‘Ka hore ni, na kuwa horu, Kamar ɗan maraƙin da ba shi da horo, Ka komo da ni don in zama kamar yadda nake a dā, Gama kai ne Ubangiji Allahna.
Sai Ubangiji ya juya ya dubi Bitrus. Bitrus kuwa ya tuna da maganar da Ubangiji ya faɗa masa cewa, “A yau ma kafin carar zakara, za ka yi musun sanina sau uku.”