48 Amma Yesu ya ce masa, “Yahuza, ashe, da sumba za ka ba da Ɗan Mutum?”
48 Amma Yesu ya tambaye shi ya ce, “Yahuda, ashe, da sumba za ka bashe Ɗan Mutum?”
Aboki aboki ne ko da ya cuce ka, amma maƙiyi ko ya rungume ka kada ka sake!
Kalmominsa sun fi mai taushi, Amma ƙiyayya tana a zuciyarsa, Kalmominsa sun fi mai sulɓi, Amma suna yanka kamar kakkaifan takobi.
Kafin ya rufe baki, sai ga taron jama'a suka zo, mutumin da ake kira Yahuza, ɗaya daga cikin sha biyun nan, yake musu jagaba. Sai ya matso kusa da Yesu, don ya sumbace shi.
Da na kusa da shi suka ga abin da za a yi, suka ce, “Ya Ubangiji, mu yi sara da takuba ne?”