Da ya ci gaba kaɗan, sai ya fāɗi a ƙasa, ya yi addu'a ya ce, “Ya Ubana, in mai yiwuwa ne, ka ɗauke mini ƙoƙon wahalar nan. Duk da haka dai ba nufina ba, sai naka.”
Sai Bafarisiyen ya miƙe, ya yi addu'a ga kansa ya ce, ‘Ya Allah, na gode maka, da yake ni ba kamar sauran mutane nake ba, mazambata, marasa adalci, mazinata, ko ma kamar mai karɓar harajin nan.
Mai karɓar haraji kuwa yana tsaye daga can nesa, bai yarda ya ɗaga kai sama ba, sai dai yana bugun ƙirjinsa, yana cewa, ‘Ya Allah, ka yi mini jinƙai, ni mai zunubi!’
Amma Bitrus ya fitar da su duka waje, ya durƙusa, ya yi addu'a. Ya juya wajen gawar, ya ce, “Tabita, tashi.” Ta buɗe ido, da ta ga Bitrus, ta tashi zaune.
Amma da lokacin tashinmu ya yi, muka tashi muka ci gaba da tafiyarmu, dukansu kuma har da matansu da 'ya'yansu, suka raka mu bayan gari, sa'an nan muka durƙusa a kan gaci, muka yi addu'a, muka yi bankwana da juna.
Almasihu, a lokacin zamansa a duniya, ya yi addu'o'i da roƙe-roƙe, tare da kuka mai tsanani, har da hawaye, ga wannan da yake da ikon cetonsa daga mutuwa, aka kuwa saurare shi saboda tsananin miƙa kansa.