Sai na ji wata murya mai ƙara a Sama tana cewa, “A yanzu fa, ceto, da ƙarfi, da mulki na Allahnmu, da kuma ikon Almasihunsa sun bayyana, don an jefa mai ƙarar 'yan'uwanmu a ƙasa, shi da yake ƙararsu dare da rana a gun Allahnmu.
“Zan umarta a rairayi jama'ar Isra'ila Da matankaɗi kamar hatsi. Zan rairaye su daga cikin sauran al'umma, Duk da haka ko ƙwaya ɗaya ba za ta salwanta ba.