21 Amma ga shi, mai bashe ni ɗin nan yana ci a akushi ɗaya da ni.
21 Amma hannun wanda zai ci amanata, yana cin abincin tare da ni.
Har da shaƙiƙin abokina, Wanda na fi amincewa da shi. Wanda muke ci tare, ya juya yana gāba da ni.
Sai Yesu ya amsa ya ce, “Shi ne wanda zan tsoma 'yar lomar nan in ba shi.” Da ya tsoma 'yar lomar kuwa, sai ya ba Yahuza, Ɗan Saminu Iskariyoti.
Aminaina na kusa sukan dube ni, duban ƙyama, Waɗanda na fi ƙaunarsu duka sun zama maƙiyana.
Da magariba ta yi, sai ya zo tare da sha biyun nan.