14 Da lokaci ya yi, sai ya zauna cin abinci, manzanninsa kuma suna tare da shi.
14 Da lokaci ya yi, sai Yesu ya zauna tare da manzanninsa don cin abinci.
Da magariba ta yi, sai ya zauna cin abinci tare da almajiran nan goma sha biyu.
Da magariba ta yi, sai ya zo tare da sha biyun nan.
Manzannin suka komo wurin Yesu, suka faɗa masa duk iyakar abin da suka yi, da abin da suka koyar.
Sai suka tafi, suka kuwa tarar kamar yadda ya faɗa musu, suka shirya Jibin Ƙetarewa.
Ya ce musu, “Ina so ƙwarai ko dā ma in ci jibin nan na Ƙetarewa tare da ku, kafin in sha wuya.