Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Luka 21:34 - Littafi Mai Tsarki

34 “Ku kula da kanku fa, kada zuciyarku ta zarme da yawan shaye-shaye da buguwa, da kuma taraddadin wannan duniya, har ba labari ranan nan ta mamaye ku kamar tarko.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

34 “Ku lura fa don kada son jin daɗi na banza, da shaye-shaye, da damuwa na rayuwa su rinjayi zuciyarku, har ranar ta auko muku ba tsammani kamar tarko.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Luka 21:34
37 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

amma taraddadin duniya, da jarabar dukiya, da kuma kwaɗayin waɗansu abubuwa, sukan shiga su sarƙe Maganar, har ta zama marar amfani.


Ku ma sai ku zauna a kan shiri, domin a lokacin da ba ku zata ba Ɗan Mutum zai zo.”


ko ɓarayi, ko makwaɗaita, ko mashaya, ko masu zage-zage, ko mazambata, da za su sami gādo a cikin Mulkin Allah.


Don haka, sai ka tuna da abin da ka karɓa ka kuma ji, ka kiyaye shi, sa'an nan ka tuba. In ba za ka yi tsaro ba, zan zo kamar ɓarawo, ba kuwa za ka san a lokacin da zan auko maka ba.


Saboda haka, ya ƙaunatattuna, tun da kuke jiran waɗannan abubuwa, ku himmantu ya same ku marasa tabo, marasa aibu, masu zaman salama.


da bautar gumaka, da sihiri, da gāba, da jayayya, da kishi, da fushi, da sonkai, da tsaguwa, da hamayya,


Sai dai na rubuta muku ne, don kada ku yi cuɗanya da duk wanda ake kira ɗan'uwa, mai bi, in yana fasikanci, ko makwaɗaici, ko matsafi, ko mai zage-zage, ko mashayi, ko mazambaci, kada ku ko ci abinci da irin waɗannan.


Wanda ya faɗa cikin ƙaya kuwa, shi ne wanda ya ji Maganar, amma taraddadin duniya da jarabar dukiya sukan sarƙe Maganar, har ta zama marar amfani.


“Karuwanci, da ruwan inabi, Da ruwan inabin da bai sa hauka ba sukan kawar da hankali.


Har da annabawa da firistoci, tangaɗi suke yi, mashaya ne. Sun sha ruwan inabi da barasa da yawa, suna ta tuntuɓe barkatai. Annabawan sun bugu ƙwarai, har ba su iya fahimtar wahayin da Allah ya aiko musu ba, firistoci su ma sun bugu, har sun kāsa yanke shari'un da aka kawo musu.


Sai ya ce, “Ku kula fa kada a ɓad da ku. Don mutane da yawa za su zo da sunana, suna cewa su ne ni, suna kuma cewa, ‘Lokaci ya yi kusa.’ To, kada ku bi su.


Kada ku damu da kome, sai dai a kowane hali ku sanar da Allah bukatunku, ta wurin yin addu'a da roƙo, tare da gode wa Allah.


Ku kula da kanku fa. In ɗan'uwanka ya yi laifi, ka tsauta masa. In kuwa ya tuba, ka yafe shi.


Amma Ubangiji ya amsa mata ya ce, “Marta, Marta! Hankalinki a tashe yake, kina kuma damuwa kan abu da yawa.


Waɗanda suka fāɗi cikin ƙaya kuwa su ne waɗanda suka ji Maganar, amma a kwana a tashi, sai yawan taraddadin duniya, da dukiya, da shagalin duniya su sarƙe su, har su kasa yin amfani.


“Amma ku kula da kanku, don za su kai ku gaban majalisa, a kuma yi muku dūka a majami'u. Za a kuma kai ku gaban mahukunta da sarakuna saboda sunana, domin ku ba da shaida a gabansu.


Girmankai da fāriya suke bi da mugaye, wannan kuwa zunubi ne.


Ku kula fa, kada kowa yă kāsa samun alherin Allah, kada kuma wani tushen ɗacin rai ya tabbata, ya haddasa ɓarna, har ya ɓata mutane masu yawa ta haka,


Amma kafin su farga, hallaka za ta kama su. Tarkunan da suka kafa za su kama su, Su kuma fāɗa cikin ramin da suka haƙa!


Abigail ta koma wurin Nabal, ta iske shi yana biki irin na sarakuna a gidansa. Ya yi ta nishaɗi, ya bugu sosai, don haka ba ta ce masa kome ba sai da safe.


Idan wani mutum ya ji zantuttukan la'anan nan sa'an nan ya sa wa kansa albarka a zuciyarsa, yana cewa, ‘Ba abin da zai same ni ko na bi taurin zuciyata,’ wannan zai haddasa lalacewar ɗanye da busasshe gaba ɗaya.


“Kada kai da 'ya'yanka maza ku sha ruwan inabi, ko abin sha mai ƙarfi sa'ad da za ku shiga alfarwa ta sujada don kada ku mutu. Wannan doka ce a dukan zamananku.


Duk da haka, ranar Ubangiji za ta zo kamar ɓarawo, sa'an nan sammai za su shuɗe da ƙara mai tsanani, dukkan abin da yake a cikinsu za su ƙone, su hallaka, ƙasa kuma da abubuwan da suke a kanta, duk za su ɓăce.


Zo dai, mu sa mahaifinmu ya sha ruwan inabi, sa'an nan sai mu kwana da shi, domin kada zuriyar mahaifinmu ta ƙare.”


Kada ka zauna da mashayan ruwan inabi, ko masu haɗama.


Gama mutum bai san lokacinsa ba, kamar kifayen da akan kama da taru, kamar kuma tsuntsayen da akan kama da tarko, haka nan mugun lokaci yakan auko wa 'yan adam farat ɗaya.


Don haka, za ta auka wa mazaunan duniya duk, kowa da kowa.


Saboda haka suka sa shi ya bugu da ruwan inabi a wannan dare kuma, ƙaramar ta shiga ta kwana da shi. Shi kuwa bai san da kwanciyarta ba balle fa tashinta.


Ya tafi ya kamo su, ya kawo su ga mahaifiyarsa, mahaifiyarsa kuwa ta shirya abinci mai daɗi irin wanda mahaifinsa yake so.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ