33 Sararin sama da ƙasa za su shuɗe, amma maganata ba za ta shuɗe ba.”
33 Sama da ƙasa za su shuɗe, amma kalmomina ba za su taɓa shuɗewa ba.
Hakika ciyawa takan bushe, furanni kuwa su yi yaushi, Amma maganar Allah ba za ta taɓa faɗuwa ba!”
Sararin sama da ƙasa za su shuɗe, amma maganata ba za ta shuɗe ba.”
Sararin sama da kasa za su shuɗe, amma maganata ba za ta shuɗe ba.”
Ku duba sammai, ku duba duniya! Sammai za su shuɗe kamar hayaƙi, Duniya kuwa za ta yage kamar tsohuwar tufa, Dukan mutanenta kuma za su mutu. Amma ceton da zan kawo zai dawwama har abada, Nasarata, ita ce za ta zama ta har abada.
Su za su ɓace duka, amma kai za ka dawwama, Za su ƙare kamar yadda tufafi suke ƙarewa, Za ka sāke su kamar tufafi, za su kuwa ɓace.
Hakika ina gaya muku, kafin sararin sama da ƙasa su shuɗe, ko wasali ko ɗigo na Attaura ba za su shuɗe ba, sai an cika dukan kome.
Maganar Ubangiji kuwa dawwamammiya ce,” Ita ce maganar bishara da aka yi muku.
Sa'an nan na ga wani babban kursiyi fari, da wanda yake a zaune a kai, sai sama da ƙasa suka guje wa Zatinsa, suka ɓace.
Tuntuni na ji labarin koyarwarka, Ka sa su tabbata har abada.
Duk da haka, zai fi sauƙi sararin sama da ƙasa su shuɗe, da ɗigo ɗaya na Attaura ya gushe.”
Hakika, ina gaya muku, zamanin nan ba zai shuɗe ba, sai duk abubuwan nan sun auku.