17 Kowa kuma zai ƙi ku saboda sunana.
17 Duk mutane za su ƙi ku saboda ni.
Da ku na duniya ne da duniya ta so abinta, amma saboda ku ba na duniya ba ne, na kuma zaɓe ku daga duniya, shi ya sa duniya take ƙinku.
“Albarka tā tabbata a gare ku sa'ad da mutane suka ƙi ku, suka kuma ware ku, suka zage ku, suka yi ƙyamar sunanku saboda Ɗan Mutum.
Saboda haka, ina murna da raunanata, da cin mutuncin da ake yi mini, da shan wuya, da shan tsanani, da masifu saboda Almasihu, don sa'ad da nake rarrauna, a sa'an nan ne nake da ƙarfi.
Duk wannan za su yi muku saboda sunana, don ba su san wanda ya aiko ni ba.
Na sani kana haƙuri, kana kuma jimiri saboda sunana, ba ka kuwa gaji ba.
Gama an yi muku alheri, cewa ba gaskatawa da Almasihu kawai za ku yi ba, har ma za ku sha wuya dominsa,
Wato, muddin muna a raye, kullum zaman mutuwa muke yi saboda Yesu, domin a bayyana ran Yesu ta wurin jikin nan namu mai mutuwa.
Na faɗa musu maganarka, duniya kuwa ta ƙi su, domin su ba na duniya ba ne, kamar yadda ni ma ba na duniya ba ne.
Kowa kuma zai ƙi ku saboda sunana. Amma duk wanda ya jure har ƙarshe zai cetu.”
“Sa'an nan za su bashe ku, a ƙuntata muku, su kuma kashe ku. Duk al'ummai za su ƙi ku saboda sunana.
Kowa kuma zai ƙi ku saboda sunana. Amma duk wanda ya jure har ƙarshe, zai cetu.
Albarka ta tabbata a gare ku in ana zaginku saboda sunan Almasihu, don Ruhun ɗaukaka, wato Ruhun Allah yā tabbata a gare ku.
Domin zan sanar da shi yawan wuyar da lalle zai sha saboda sunana.”
Ba dama duniya ta ƙi ku, amma ni take ƙi, don na shaide ta a kan ayyukanta mugaye ne.
“Albarka tā tabbata gare ku sa'ad da mutane suka zage ku, suka tsananta muku, suka kuma ƙaga muku kowace irin mugunta, saboda ni.
Domin ba wa'azin kanmu muke yi ba, sai dai na Yesu Almasihu a kan shi ne Ubangiji, mu kuwa bayinku ne saboda Yesu.
Ko da iyayenku ma da 'yan'uwanku, da danginku, da abokanku, sai sun bāshe ku, su kuma sa a kashe waɗansunku.
Amma ba gashin kanku ko ɗaya da zai yi ciwo.