41 Amma ya ce musu, “Ƙaƙa za su ce Almasihu ɗan Dawuda ne?
41 Sai Yesu ya ce musu, “Yaya suke cewa, ‘Kiristi ɗan Dawuda ne?’
Littafin asalin Yesu Almasihu, ɗan Dawuda, zuriyar Ibrahim ke nan.
To, da yake shi annabi ne, ya kuma san Allah ya rantse masa, cewa zai ɗora wani daga cikin zuriya tasa kan kursiyinsa,
Nassi ba cewa ya yi Almasihu zuriyar Dawuda ne ba, daga kuma Baitalami yake, ƙauyen da Dawuda ya zauna?”
“Ni Yesu, na aiko mala'ikana a gare ka, da wannan shaida saboda ikilisiyoyi. Ni ne tsatson Dawuda, da zuriyarsa, Gamzaki mai haske.”
to, ashe, alkawarin da na yi wa bawana Dawuda zai tashi ke nan, har ya rasa ɗan da zai yi mulki a gadon sarautarsa, alkawarin kuma da na yi wa firistoci masu yi mini hidima, da ma'aikatana, zai tashi.
Da Yesu ya yi gaba daga nan, sai waɗansu makafi biyu suka bi shi, suna ɗaga murya suna cewa, “Ya Ɗan Dawuda, ka ji tausayinmu.”