39 Sai waɗansu malaman Attaura suka amsa suka ce, “Malam, ka faɗi daidai.”
39 Sai waɗansu malaman dokoki suka amsa suka ce, “Ka faɗi daidai, malam!”
Sai ƙasaitacciyar hargowa ta tashi, waɗansu malamai kuma na ɗariƙar Farisiyawa suka miƙe a tsaye, suka yi ta yin matsananciyar jayayya, suna cewa, “Mu ba mu ga laifin mutumin nan ba. In wani ruhu ne ko mala'ika ya yi masa magana fa?”
Ai, waɗanda Allah shi ne Allahnsu rayayyu ne, ba matattu ba. Don a wurinsa duka rayayyu ne.”
Daga nan kuma ba su yi ƙarfin halin tambayarsa wani abu ba.