34 Sai Yesu ya ce musu, “Mutanen zamanin nan suna aure, suna aurarwa.
34 Yesu ya amsa ya ce, “Mutanen zamanin nan suna aure, suna kuma ba da aure,
Sai maigidan ya yaba wa wakilin nan marar gaskiya saboda wayonsa. Don 'yan zamani a ma'ammalarsu da mutanen zamaninsu, sun fi mutanen haske wayo.
Ana ci, ana sha, ana aure, ana aurarwa, har ya zuwa ranar da Nuhu ya shiga jirgi, Ruwan Tsufana kuma ya zo, ya hallaka su duka.
Kowa yă girmama aure, Gădon aure kuwa yă zauna marar dauɗa, don fasikai da mazinata Allah zai hukunta su,
“Saboda haka ne, mutum sai ya bar mahaifinsa da mahaifiyarsa, ya manne wa matarsa, su biyu su zama jiki guda.”
Kowa ya aibata Ɗan Mutum, ā gafarta masa. Amma wanda ya aibata Ruhu Mai Tsarki, ba za a gafarta masa ba, duniya da lahira.”
To, a tashin matattu, matar wa za ta zama a cikinsu? Don duk bakwai ɗin sun aure ta.”