32 Daga baya kuma ita matar ta mutu.
32 A ƙarshe, ita macen ma ta mutu.
Hakika rayayyu sun san za su mutu, amma matattu ba su san kome ba. Ba su da wani sauran lada nan gaba, an manta da su ke nan sam.
Zamani yakan wuce, wani zamani kuma ya zo, Amma abadan duniya tana nan yadda take.
Tun da yake an ƙaddara wa ɗan adam ya mutu sau ɗaya ne, bayan haka kuma sai shari'a,
Dukan tsarar Joshuwa sun rasu, waɗanda suke tasowa kuwa suka manta da Ubangiji da abubuwan da ya yi wa Isra'ila.
da na ukun kuma suka aure ta. Haka dai, duk bakwai ɗin suka aure ta, suka mutu, ba wanda ya bar ɗa.
To, a tashin matattu, matar wa za ta zama a cikinsu? Don duk bakwai ɗin sun aure ta.”