Amfanin ƙasa duk yana tafiya ga sarakunan Da ka ɗora su a kanmu saboda mun yi zunubi. Suna yi mana yadda suka ga dama, mu da dabbobinmu, Muna cikin baƙin ciki.”
Bayansa kuma, a lokacin ƙirgen mutane, wai shi Yahuza Bagalile ya ɓullo, ya zuga waɗansu suka yi turu, suka bi shi. Shi ma ya hallaka, duk mabiyansa ma aka warwatsa su.
Ya ce, “I, yakan bayar.” Da ya dawo gida kuma, sai Yesu ya fara yi masa magana ya ce, “Me ka gani, Bitrus? Wurin wa sarakunan duniya suke karɓar kuɗin fito ko haraji, a wurin 'ya'yansu, ko kuwa daga wurin waɗansu?”
Tun daga zamanin kakanninmu muna da babban laifi. Saboda zunubanmu, mu da sarakunanmu, da firistocinmu, aka bashe mu a hannun sarakunan waɗansu ƙasashe, aka bashe mu ga takobi, aka kai mu bauta, aka washe mu, aka kunyatar da mu kamar yadda yake a yau.
Sarki ya sani fa, idan an sāke gina birnin, aka kuma gama garun, ba za su biya haraji ko kuɗin shiga da fita na kaya ko kuɗin fito ba, baitulmalin sarki za ta rasa kuɗi ke nan.
to, kwā iya naɗa wa kanku sarki wanda Ubangiji Allahnku ya zaɓa. Sai ku naɗa wa kanku sarki daga cikin jama'arku. Kada ku naɗa wa kanku baƙo wanda ba ɗan'uwanku ba.
Suka tambaye shi suka ce, “Malam, ai, mun sani maganarka da koyarwarka duk gaskiya ne. Ka ɗauki kowa da kowa daidai, sai koyar da tafarkin Allah sosai kake yi.
Sai suka fara kai ƙararsa, suna cewa, “Mun sami mutumin nan yana ɓad da jama'armu, yana hana a biya Kaisar haraji, yana cewa, shi ne Almasihu, sarki kuma.”
Ku ba kowa hakkinsa, masu haraji, harajinsu, masu kuɗin fito, kuɗinsu na fito, waɗanda suka cancanci ladabi, ladabi, waɗanda suka cancanci girmamawa, girmamawa.