Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Luka 2:4 - Littafi Mai Tsarki

4 Yusufu shi ma ya tashi daga birnin Nazarat, a ƙasar Galili, ya tafi ƙasar Yahudiya, ya je birnin Dawuda, da ake kira Baitalami (domin shi daga gidan Dawuda ne, na cikin zuriyarsa),

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

4 Saboda haka Yusuf ma ya haura daga Nazaret a Galili zuwa Yahudiya, ya tafi Betlehem garin Dawuda, don shi daga gida da kuma zuriyar Dawuda ne.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Luka 2:4
24 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

“Baitalami cikin Efrata, Wadda kike 'yar ƙarama a cikin kabilar Yahuza, Amma daga cikinki wani zai fito wanda zai sarauci Isra'ila Wanda asalinsa tun fil azal ne.”


Nassi ba cewa ya yi Almasihu zuriyar Dawuda ne ba, daga kuma Baitalami yake, ƙauyen da Dawuda ya zauna?”


Ubangiji ya ce wa Sama'ila, “Har yaushe za ka yi ta ɓacin rai saboda Saul? Ga shi kuwa, na ƙi shi da zama Sarkin Isra'ila. Ka sami man zaitun ka ɗauka. Zan aike ka zuwa wurin Yesse mutumin Baitalami, gama na zaɓi ɗaya daga cikin 'ya'yansa maza ya zama sarki.”


Ya zo Nazarat inda aka rene shi. Ya shiga majami'a a ran Asabar kamar yadda ya saba. Sai ya miƙe domin ya yi karatu.


Sai ya je ya zauna a wani gari wai shi Nazarat, domin a cika faɗar annabawa cewa, “Za a kira shi Banazare.”


Idan mahaifinka bai gan ni ba, sai ka ce masa, ni na roƙe ka ka bar ni in gaggauta zuwa Baitalami, garinmu, domin akwai ba da sadaka ta shekara saboda dukan gidanmu.


Mata, maƙwabta kuwa suka ce, “An haifa wa Na'omi ɗa!” Suka raɗa masa suna Obida, shi ne mahaifin Yesse, uban Dawuda.


Dukan jama'a suka ce, “Mu ne shaidu, Ubangiji yă sa matar da za ta zo gidanka ta zama kamar Rahila da Lai'atu waɗanda suka gina gidan Isra'ila. Allah ya arzuta ka cikin Efrata, yă sa ka yi suna a cikin Baitalami,


Sai ga Bo'aza ya zo daga Baitalami, ya ce wa masu girbi, “Salamu alaikun.” Suka amsa, “Alaika salamu.”


Nata'ala ya ce masa, “A iya samun wani abin kirki a Nazarat kuwa?” Sai Filibus ya ce masa, “Taho dai, ka gani.”


Saul ya tambayi Dawuda, ya ce, “Saurayi, kai ɗan wane ne?” Dawuda ya amsa, ya ce, “Ni ɗan baranka ne, Yesse, mutumin Baitalami.”


Dawuda kuwa ɗan Yesse ne, wanda yake mutumin Efrata, ta Baitalami cikin Yahuza, yana da 'ya'ya maza guda takwas, ya kuwa riga ya tsufa a zamanin Saul.


Sama'ila ya yi yadda Ubangiji ya faɗa masa, ya tafi Baitalami, inda dattawan garin suka tarye shi da rawar jiki, suka ce masa, “Maigani, wannan ziyara lafiya kuwa?”


Su biyu kuwa suka kama hanya har suka isa Baitalami. Da suka isa Baitalami, sai dukan garin ya ruɗe saboda su. Mata suka ce, “Na'omi ce wannan?”


Sa'ad da nake zuwa daga Mesofotamiya, sai Rahila ta rasu a hannuna a ƙasar Kan'ana a kan hanya, ga shi kuwa, da sauran tazara kafin a kai Efrata. Na kuwa binne ta a Efrata,” wato Baitalami.


Ta haka fa Rahila ta rasu, aka kuwa binne ta a bakin hanya zuwa Efrata, wato Baitalami.


Amma tun yana cikin wannan tunani, sai ga wani mala'ikan Ubangiji ya bayyana a gare shi a mafarki, ya ce, “Yusufu ɗan Dawuda, kada ka ji tsoron ɗaukar Maryamu matarka, domin cikin nan nata daga Ruhu Mai Tsarki ne.


don a rubuta shi, duk da Maryamu tashinsa, wadda take kuma da ciki.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ