Da suka gan shi suka yi mamaki, sai uwa tasa ta ce masa, “Ya kai ɗana, yaya ka yi mana haka? Ga shi nan, ni da babanka muna ta nemanka duk ranmu a ɓace.”
Ga ni tare da 'ya'yan da Ubangiji ya ba ni. Ubangiji Mai Runduna, wanda kursiyinsa a kan Dutsen Sihiyona yake, ya maishe mu rayayyen jawabi ga jama'ar Isra'ila.
Da Yesu ya ji haka, sai ya yi mamaki, har ya ce wa mabiyansa, “Gaskiya, ina gaya muku, ko a cikin Isra'ila ban taɓa samun bangaskiya mai ƙarfi irin wannan ba.