Ubangiji ya ce mini, “Bawana, ina da aiki mai girma dominka, Ba komo da girman jama'ar Isra'ila da suka ragu kaɗai ba, Amma zan sa ka zama haske ga al'ummai, Domin dukan duniya ta tsira.”
“Rana ba za ta ƙara zama haskenki da rana ba, Ko wata ya zama haskenki da dare. Ni, Ubangiji, zan zama madawwamin haskenki, Hasken ɗaukakata zai haskaka a kanki.
Lokaci na zuwa sa'ad da Ubangiji zai sa kowane tsiro da kowane itacen da take a ƙasar su girma su yi kyau. Dukan jama'ar Isra'ila waɗanda suka ragu za su yi fāriya, su yi murna saboda amfanin da ƙasar take bayarwa.
Rana tana zuwa sa'ad da sabon sarki zai fito daga cikin gidan sarautar Dawuda, zai zama alama ga sauran al'umma. Za su tattaru a birnin sarautarsa su girmama shi.
Zan ce wa 'yan kurkuku, ‘Ku tafi na sake ku!’ Waɗanda suke cikin duhu kuwa, in ce musu, ‘Ku fito zuwa wurin haske!’ Za su zama kamar tumakin da suke kiwo a tuddai,