30 Don na ga cetonka zahiri,
30 Gama idanuna sun ga cetonka,
Dukkan 'yan adam kuma za su ga ceton Allah.”
Ubangiji ya ce mini, “Bawana, ina da aiki mai girma dominka, Ba komo da girman jama'ar Isra'ila da suka ragu kaɗai ba, Amma zan sa ka zama haske ga al'ummai, Domin dukan duniya ta tsira.”
Ubangiji ya nuna ikonsa mai tsarki, Ya ceci jama'arsa, Dukan duniya kuwa ta gani.
Ina zuba ido ga cetonka, ya Ubangiji.
Ina jiranka ka cece ni, ya Ubangiji, Ina aikata abin da ka umarta.
Ina sa zuciya ga cetonka ƙwarai, ya Ubangiji! Ina samun farin ciki ga dokarka.
Da ka shirya a gaban kabilai duka,
To, sai ku sani, wannan ceto na Allah, an aiko da shi har ga al'ummai, su kam za su saurara.”