Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Luka 2:2 - Littafi Mai Tsarki

2 Wannan shi ne ƙirga na fari da aka yi a zamanin Kiriniyas, mai mulkin ƙasar Suriya.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

2 (Wannan ce ƙidaya ta fari da aka yi a lokacin da Kwiriniyus yake gwamnar Suriya.)

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Luka 2:2
9 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

A shekara ta goma sha biyar ta mulkin Kaisar Tibariyas, Buntus Bilatus yana mulkin Yahudiya, Hirudus yana sarautar Galili, ɗan'uwansa Filibus yana sarauta Ituriya da Tarakunitas, Lisaniyas kuma yana sarautar Abiliya,


Sai sarki ya tashi, haka kuma mai mulki da Barniki, da waɗanda suke a zaune tare da su.


“Daga Kalaudiyas Lisiyas zuwa ga mafifici mai mulki Filikus. Gaisuwa mai yawa.


Amma sa'ad da Galiyo yake muƙaddashin ƙasar Akaya, Yahudawa suka tasar wa Bulus da nufi ɗaya suka kawo shi a gaban shari'a,


Wanda yake tare da muƙaddas Sarjiyas Bulus, mutum mai basira. Sai muƙaddashin ya kira Barnaba da Shawulu ya nemi jin Maganar Allah.


Bayansa kuma, a lokacin ƙirgen mutane, wai shi Yahuza Bagalile ya ɓullo, ya zuga waɗansu suka yi turu, suka bi shi. Shi ma ya hallaka, duk mabiyansa ma aka warwatsa su.


Ta haka ya shahara a cikin duk ƙasar Suriya. Aka kuwa kakkawo masa dukan marasa lafiya, masu fama da cuta iri iri, da masu shan azaba, da kuma masu aljannu, da masu farraɗiya, da shanyayyu, ya kuwa warkar da su.


A kwanakin nan Kaisar Augustas ya yi shela, cewa a rubuta dukkan mutanen da suke ƙarƙashin mulkinsa.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ