19 Maryamu kuwa sai ta riƙe duk abubuwan da aka faɗa, tana biya su a zuci.
19 Amma Maryamu ta riƙe dukan waɗannan abubuwa ta kuma yi ta tunaninsu a zuciyarta.
Sai ya koma Nazarat tare da su, yana yi musu biyayya. Uwa tasa kuwa na riƙe da dukan abubuwan nan a ranta.
Duk waɗanda suka ji kuwa suka riƙe a zuciyarsu, suna cewa, “Me ke nan ɗan yaron nan zai zama?” Gama ikon Ubangiji yana tare da shi.
mahaifina yakan koya mini, yakan ce, “Ka tuna da abin da nake faɗa maka, kada ka manta. Ka yi abin da na faɗa maka za ka rayu.
Da Dawuda ya ji waɗannan maganganu, sai ya tsorata ƙwarai da Akish Sarkin Gat.
Duk wanda yake da hikima, bari ya fahimci abubuwan nan. Duk wanda yake da ganewa, bari ya san abubuwan nan, Gama hanyoyin Ubangiji masu gaskiya ne, Masu adalci kuwa za su yi tafiya a cikinsu, Amma masu zunubi za su yi tuntuɓe a kansu.
'Yan'uwansa suka ji kishinsa, amma mahaifinsa ya riƙe al'amarin cikin zuciyarsa.
Na riƙe maganarka a zuciyata, Don kada in yi maka zunubi.
“Ni Daniyel na firgita ƙwarai, fuskata ta yi yaushi. Amma na riƙe al'amarin duka a zuciyata.”
Duk waɗanda suka ji kuma, suka yi ta al'ajabin abin da makiyayan nan suka faɗa musu.