Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Luka 19:5 - Littafi Mai Tsarki

5 Da Yesu ya iso wurin, ya ɗaga kai ya ce masa, “Zakka, yi maza ka sauko, domin yau lalle a gidanka zan sauka.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

5 Da Yesu ya iso wurin, sai ya ɗaga ido sama, ya ce masa, “Zakka, ka yi maza ka sauka. Ni kam, dole in sauka a gidanka yau.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Luka 19:5
17 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ga ni nan a tsaye a bakin ƙofa, ina ƙwanƙwasawa, kowa ya ji muryata ya buɗe ƙofar, sai in shiga wurinsa, in ci abinci tare da shi, shi kuma tare da ni.


Yesu ya amsa masa ya ce, “Kowa yake ƙaunata, zai kiyaye maganata, Ubana kuwa zai ƙaunace shi, za mu zo wurinsa mu zauna tare da shi.


Kada ku daina yi wa baƙi alheri, gama ta haka ne waɗansu suka sauki mala'iku ba da sani ba.


Nata'ala ya ce masa, “A ina ka san ni?” Yesu ya amsa masa ya ce, “Tun kafin Filibus ya kira ka, sa'ad da kake gindin ɓaure, na gan ka.”


har ma Almasihu yă zauna a zukatanku ta wurin bangaskiyarku, domin ƙauna ta kahu da gindinta sosai a zukatanku,


Don Ɗan Mutum ya zo ne musamman garin neman abin da ya ɓata, yă cece shi kuma.”


“Sa'ad da na wuce kusa da ke, na gan ki kina birgima cikin jinin haihuwarki, sai na ce miki lokacin da kike cikin jinin, ‘Ki rayu!’ I, na ce miki lokacin da kike cikin jinin, ‘Ki rayu!’


Duk abin da kake iya yi, ka yi shi da iyakar iyawarka, domin ba aiki, ko tunani, ko ilimi, ko hikima a lahira, gama can za ka.


Da yake kuma muna aiki tare da Allah, muna roƙonku kada ku yi na'am da alherin Allah a banza.


sai wani mutum mai suna Zakka, babba ne a cikin masu karɓar haraji, mai arziki ne kuma,


Sai ya yi gaba a guje, ya hau wani durumi don ya gan shi, don Yesu ta nan zai bi.


Sai ya yi hanzari ya sauko, ya karɓe shi da murna.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ