Amma ni ban yi gudun zaman makiyayi a gabanka ba, Ban kuma so zuwan ranar bala'i ba, Ka kuwa sani. Abin da ya fito daga bakina kuwa, A bayyane yake gare ka.
Amma idan ba za ku ji ba, Raina zai yi kuka a ɓoye saboda girmankanku, Idanuna za su yi kuka ƙwarai, za su zub da hawaye, Domin an kai garken Ubangiji zuwa bauta.
“Ƙaƙa zan iya rabuwa da ke, ya Ifraimu? Ƙaƙa zan miƙa ki, ya Isra'ila? Ƙaƙa zan maishe ki kamar Adma? Ƙaƙa zan yi da ke kamar Zeboyim? Zuciyata tana motsawa a cikina, Juyayina ya huru.
Ubangiji zai yi yaƙi kamar yadda ya yi a Dutsen Ferazim da a Kwarin Gibeyon domin ya aikata abin da ya yi nufin yi, ko da yake ayyukansa suna da ban al'ajabi. Zai gama aikinsa, wannan aiki kuwa mai ban al'ajabi ne.