36 Yana cikin tafiya, sai mutane suka shisshimfiɗa mayafansu a hanya.
36 Yana cikin tafiya, sai mutane suka shimfiɗa rigunarsu a kan hanya.
Sai kowane mutum a cikinsu ya yi maza ya tuɓe rigarsa, ya shimfiɗa a kan matakan, sa'an nan suka busa ƙaho, suna cewa, “Yehu ne sarki.”
Yawancin jama'a suka shisshimfiɗa mayafansu a hanya, waɗansu kuma suka kakkaryo ganye suna bazawa a hanya.
Sai suka kawo shi wurin Yesu. Da suka shimfiɗa mayafansu a kan aholakin, suka ɗora Yesu.
Da ya zo gab da gangaren Dutsen Zaitun, sai duk taron almajiran suka ɗauki murna, suna yabon Allah da murya mai ƙarfi saboda duk mu'ujizan da suka gani.