16 Sai na farko ya zo gabansa, ya ce, ‘Ya ubangiji, fam ɗinka ya jawo fam goma.’
16 “Na fari ya zo ya ce, ‘Ranka yă daɗe, minarka ya sami ribar goma.’
Amma saboda alherin Allah na zama yadda nake, alherin da ya yi mini kuwa ba a banza yake ba. Har ma na fi kowannensu aiki, ba kuwa ni ba, alherin Allah ne da yake zuciyata.
Sai ya kira bayinsa goma, ya ba su fam guda guda, ya kuma ce musu, ‘Ku yi ta jujjuya su har in dawo.’
Ana nan, da ya samo sarautar ya dawo, sai ya yi umarni a kirawo bayin nan da ya bai wa kuɗin, ya ga ribar da suka ci a wajen jujjuyawar.
Sai shi kuma ya ce masa, ‘Madalla, bawan kirki! Tun da ka yi gaskiya a kan ƙaramin abu, to, na ba ka mulkin gari goma.’