Luka 19:14 - Littafi Mai Tsarki14 Amma mutanensa suka ƙi shi, har suka aiki jakadu a bayansa, cewa ba sa so ya yi mulki a kansu. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202014 “Amma talakawansa suka ƙi shi, sai suka aikar da wakilai bayansa, domin su ce, ‘Ba mu son wannan mutum ya zama sarkinmu.’ အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Allah Mai Tsarki na Isra'ila, Mai Fansa, Ya ce wa wanda aka raina ƙwarai, Al'ummai suka ƙi shi, Bawa na masu mulki kuma, “Sarakuna za su gan ka a sake, Su kuma miƙe tsaye su ba ka girma, Shugabanni su kuma za su gani, Su rusuna har ƙasa su ba ka girma.” Wannan kuwa zai faru saboda Ubangiji, Allah Mai Tsarki na Isra'ila, ya zaɓi bawansa, Ya kuwa cika alkawaransa.